ungiyar NGF ta gwamnonin Najeriya ta gayyaci Gwamnan babban banki na kasa, Godwin Emefiele zuwa wani taro na musamman a gobe.

Manema labarai sun ruwaito cewa gwamnonin jihohi za su yi taron da gwamnan na CBN ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Junairu 2023 ta kafar sadarwa ta yanar gizo.
Makasudin tattaunawar ita ce Godwin Emefiele ya yi bayanin abin da ya sa babban bankin Najeriya watau CBN ya canza wasu takardun kudin kasar.

Baya ga haka, Gwamnan zai samu damar yi wa Gwamnonin jihohin karin haske game da tsarin da aka fito da shi na takaita cire kudi a bankuna.

shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bada wannan sanarwa ranar a ranar Talata.
Kungiyar NGF ta ce zaman zai bada damar ganawa tsakanin masu ruwa da tsaki daga bangaren gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.
Tun bayan da babban bankin da Godwin Emefiele yake jagoranta ya canza takardun kudi, ya kuma rage adadin kudin za a iya cirewa a kullum, ake ta surutai.