Dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Tinubu, yayi kira ga ‘yan Najeriya da kar su bar jam’iyyar PDP ta dawo kan madafun iko.

Ya bayyana hakan ne jiya a Jihar Jigawa, wajen gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a filin taro na Malam Aminu Kano dake Birnin Dutse.

Da yake bayani ga Babban taron jama’ar Wurin ya bayyana cewa, sakamon korar kuraye da aka yi a shekarar 2015. Zai zama Babbar Annoba idan aka bari suka dawo Mulki.

Ya kara da cewa, kunyi babban aiki Na korar su shekaru takwas da suka gabata, kar Ku yarda da Alkawuransu Na Yaudara, kar Ku bari su dawo mulki.

Ya kuma kara da cewa idan har suka zabe shi, gwamnatinsa zata cigaba akan ayyukan Shugaba Buhari. Dan kasar ta kuma Ingantuwa.

A tsare-tsaren sa yayi Alkawarin cewa, zasu kara inganta fannin noma. Sannan su kuma mayar da Hankali ga ayyukan more rayuwa a kasar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Tinubu ya kuma bukaci yan Jihar Jigawa, da su zabi shugabanni Na gari da suka dace a zaben da za’a yi a watan Fabarairu da Maris masu zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: