Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, ya shawarci ‘yan Najeriya da kar su yi kuskuren sake zabar jam’iyya mai mulki ta APC a zabe mai ‘karatowa.

Ya bayyana cewa, kamar cigaba da dabbaka lalataccen shugabanci ne. Idan har aka sake zaben APC ta cigaba da mulki.

Gwamnan ya bukaci dukkansu da su fito su zabi jam’iyyar PDP, domin tabbatad da nasarar jam’iyyar.

Diri ya fadi hakan ne a Gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa, lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin yakin Neman zabensa Na mazabu. Da suka kai masa ziyarar jaddada goyon baya a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ta bakin mataimakin gwamnan Ewhrudjakpo Wanda ya wakilci gwamnan yace, duk Wanda yake son Najeriya ba zai kuma zabar APC ba. La’akari da irin lalataccen shugabanci da take yi tsawon shekaru bakwai.

Ya kuma cewa, APC ta lalata Najeriya saboda haka ba zasu kara yarda da ita ba. Dan haka a zabi jam’iyyar PDP a dukkan matakai.

Jagoran kwamitin yakin Neman zaben Na mazabu Ogidi Bara-Ben shima yace, sun gamsu da kokarin da gwamnan yake yi a fadin jihar, musamman cigaba da Samar da Babban titin mazabar sanatoriyar Bayelsa ta tsakiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: