Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta kashe Dala Miliyan 150 Dan magance matsalar Zaizayar kasa da Ambaliyar ruwa a sassa daban-daban Na jihar.

Gwamnan ya fadi hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da Hukumar kula da Ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a Birnin Benin a karshen makon da ya gabata.

Mai bada shawara a harkar sadarwa Na musamman ga gwamnan Crusoe Osagie a bayanin da ya bawa Kamfanin dillancin labarai Na kasa NAN ya bayyana cewa, Obaseki zai tabbatar da kokarin gwamnatin Na shawo kan wadannan matsalolin Na Muhalli.

Obaseki ya kuma kokanta cewa, da yawan matsalolin Muhallin da suke fama dasu suna faruwa ne sakamakon sakacin Mutane.

Ya kara da cewa suna daukar kwararan matakai na kawo cigaba Jihar Dan farfadowa daga sauyin yanayi, da cigaban Muhalli da Tattalin Arziki.

Obasekin yace a tsawon shekaru Goma da suka gabata, sun kashe sama da Dala Miliyan 150 Dan gyara abubuwan da jama’a suka lalata da Kansu.

Jaridar Punch ta ruwaito Obaseki yana cewa, ginshikin su Na farko shine Muhalli, Dan ba zasu cigaba da rayuwa a yadda suke ba a yanzu.

Ya kuma ce Muhalli waje ne mai Muhimmanci da za’a mai da hankali kansa, kuma sakamakon kin bashi Muhimmanci ya sanya suka tsinci Kansu a halin da suke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: