Asusun tallafawa kananan yara na majalissar dinkin Duniya UNICEF yace, kaso 75 na yaran Najeriya ‘yan shekaru 7 zuwa 14 ba zasu iya karanta Jimla ko warware Dan karamin lissafi ba.

Wakilin UNICEF a Najeriya Cristian Munduate shi ya bayyana haka, a jawabinsa yau Talata na Ranar Ilimi ta Duniya.

Sannan kuma ya bukaci yan takarar shugabncin kasar nan, da su sanya Ilimi a abinda zasu fi bawa fifiko a zaben da yake gabatowa.

Jaridar Punch ta ruwaito shi a cikin jawabin nasa yana cewa, kaso 75 na yaran Najeriya yan tsakanin shekaru 7 zuwa 14 ba zasu iya karanta jimla ko warware Dan karamin lissafi ba.

Ya kuma ce idan ana son yaro ya iya karatu da koyo, dole sai sun koyi karatu a shekaru ukunsu na farko da fara Makaranta.

A karshe yace yadda zaben shugaban kasa ya gabato, a madadin UNICEF da yaran Najeriya, yana kira ga yan takarar shugabancin kasa da su sanya kudurin bawa Ilimi fifiko a cikin manufofinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: