Rahotanni daga ƙaramar hukumar Guzamala a jihar Borno sun tabbatar da cewar wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne sun raba tsofaffin kuɗi ga matafiya a babbar hanyar.

Al’amarin ya faru a ranar Asabar a babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno.

Wani shida da ya tabbatarwa da jaridar Dailyu Trust cewar, mayaƙan sanye da kayan sojoji sun tare babbar hanyar tare da motocin yaƙi.

Wani mazaunin garin mai suna Bakura Ibrahim ya ce mayaƙan sun rabawa matafiyar tsofaffin kuɗi da ake shirin daina karɓa nan da kwana goma.

Ya ce kowanne matafiyi sun a bashi naira dubu dari na tsofaffin kuɗi da aka sayawa fasali.

Sannan mayaƙan sun bai wa matafiyan zaɓi idan sun so zuwa banki domin sauya takardun kuɗin zuwa sababbin da aka sauya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: