Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana ra’ayinsa game da lamarin sauya fasalin Naira da ake kai ruwa rana kansa.

Ado Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Tudun Wada da Doguwa ya ce Gwamnan bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, kawai rufa-rufa ya yiwa Shugaba Buhari.


Ya ce alamu sun nuna shugaban kasan bai fahimci lamarin ba kawai shigo-shigo ba zarfi aka yi masa.
Doguwa ya bayyana hakan ne a ranar Litnin a shirin Politics Today na ChannelsTV.
Doguwa ya ce Emefiele bai yiwa Buhari bayanin da ya kamata ba kafin ya amince da lamarin sauya fasalin kudin.
Ya ce la’alla an bijirowa shugaban kasa da bayanin da bai fahimci tasirinsa ba, saboda haka dole ya yanke gurguwar shawara akan lamarin.
Doguwa ya ce ya gana da shugaba Buhari ranar Lahadi kuma ya nuna masa bacin ransa kan Gwamnan CBN, Godwin Emefiele wanda ya ki amsa gayyatar da majalisar tayi masa.
Ado Doguwa yace wata hujjar dake nuna cewa shugaba Buhari bai fahimci lamarin ba tun farko shine dage wa’adin daina amfani da tsaffin kudin da yayi da kwanaki 10.