Wasu mahara a Jihar Ebonyi sun kaiwa ayarin motocin dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA hari a Jihar ta Ebonyi.

 

Jaridar Punch ta rawaito cewa maharan sun kai wa ayarin motocin harin ne a daren ranar Alhamis.

 

Hadimin gwamnan kan yada labarai Charles Otu ne ya tabbatar da haka, inda ya ce batagarin sun kai wa ayarin motocin hari ne a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta dawowa daga yakin neman zabensa da ke kan babban hanyar Enugu zuwa Abakali.

 

Otu ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun ajiye motar su akan hanya inda su ka budewa ayarin motocin wuta da nufin harbin gwamnan.

 

A yayin harin maharan sun hallaka direban gwamnan tare da jikkata jami’an tsaron da ke tsaron lafiyar sa.

 

Kakakin ya ce wadanda su ka jikkata an kaisu Asibiti domin kula da lafiyar su.

 

Sannan ya kara da cewa daga cikin ‘yan tawagar gwamnan akwai wadanda har hawo yanzu ba a gansu ba.

 

Otu ya ce yan bindiga sun kuma kona mota daya daga cikin motocin tawagar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: