Gwamnan Jihar Abia Ooezie Pieazu ya haramta gasa kifi da wasu dabbobi da kuma yin girki a cikin kasuwannin Jihar.

Kwamishinan kasuwanci da saka hannun Jari na Jihar Cif John Okiyi Kalu shine ya bayyana hakan.

Kwamishinan ya ce Matakin ya biyo bayan wata gobara da ta tashi a ranar takwas ga watan Fabrarun da muke ciki a wata kasauwa, wanda hakan yayi sanadiyar konewar shaguna biyu.

Bayan afkuwar lamarin gwmnan Jihar ya bai’wa ma’aikatan kasuwancin da saka hannun jari da gudanar da binciken irin asarar da aka yi tare da tallafa musu.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga shugabanni kasuwanni da su da su aiwatar da dokar domin dakilai tashin gobara da ajiye abinda zai hadda gobarar tare da raba na’urar kashe gobara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: