Mikel Arteta ya bukaci Arsenal ta sa kwazo ta lashe Premier League na bana, mai makon zaman jiran hukuncin da za a yi wa Manchester City.

 

Arsenal tana matakin farko a kan teburi da tazarar maki biyar tsakaninta da City, wadda take ta biyu.

 

Ranar Laraba Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester City a kwantan wasan mako na 12 a gasar Premier League a Emirates.

 

Ranar Asabar za a fara karawar mako na 23, wani batun da ke jan hankali shi ne tuhumar City da ake da karya doka sama da 100 da ta shafi Financial Fair Play.

 

City ta musamta aikata rashin gaskiya, amma tana fuskanta hukunci da yawa idan har aka sameta da laifi.

 

Watakila a kwashe mata maki ko korarta daga Premier ko cin tara da sauransu, sai dai Arteta na fatan Arsenal ta kalubalanci lashe kofin a fili ba a siyasance ba.

 

Kafin Arsenal ta karbi bakuncin City ranar Laraba, za ta kara da Brentford a gasar Premier League a Emirates ranar Asabar.

 

City ce ta fitar da Arsenal daga FA Cup na bana da cin 1-0, sai kuma Eerton ta doke Gunners 1-0 a Premier, wasa na biyu da ta yi rashin nasara a gasar a bana.

 

Arteta ya koma jan ragamar Arsenal ranar 23 ga watan Disambar 2019 daga Manchester City, bayan da ya yi mataimakin Pep Guardiola

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: