Dan majalisa mai wakiltar Niger ta gabas Sani Musa ya jajantawa hukumar yan sanda tare da sauran iyalan Jami an yan sandan da suka rasa rayukansu a jiya a sakamakon wata fafatawa tsakanin su da yan bindiga.

Sani Musa yayi taaziyar jami’an biyar na yan sanda da baturen yan sanda wadanda aka hallaka a jiya Lahadi yayin da wasu da ake zargin yan bindiga su ka kai hari a babbar hanyar zuwa Suleja.
Cikin taaziyar da ya bayyana ya ce dole zai tabbatar da wadanda suka yi hakan ba su tsere ba an kamasu tare da gurfanar da su a gaban Shari a domin girbar abinda su ka shuka.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar yan sanda na jihar DSP Wasiu Abiodin ya bayyana ya ce wasu yan bindiga a jiya Lahadi sun kai hari kauyen kwakuti dake karamar hukumar Faikoro inda aka samu musayar wuta tsakanin su da Jami an su na yan sanda na tsawon lokaci.

Ya cigaba da cewa a yayin fatawar ne aka samun damar hallaka jami’ansu na yan sanda biyar ciki harda baturen yan sanda wato muktar Sabiu.
Abiodin ya ci gaba da cewa jami an yan sanda na cigaba da sintiri a wannan yankin duk da yankin ya na cikin kulawar jamian tsaro.
Sannan ya ce suna cigaba da aiki da kwararru domin kamo tare da tabbatar an hukunta wadanda su ka yi wannan aika aikar.