Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC Bola Tinubu yace, kudirinsa in ya zama shugaban kasa shine cigaba da hakar man fetir a jihar Gombe Dan amfanuwar yankin da kasa baki daya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a fadar sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar na uku, yayin da kwamitin yakin neman zabensa suka kai ziyarar Neman goyon baya ga sarkin.
Dan takarar na APC ya ziyarci fadar ne kafin ya wuce babban filin wasa na Pantami, yayin da dubunnan magoya bayansa da ‘yan jam’iyyar suka tarbe shi.

Ya bayyana cewa, zai tabbatar da martabar Gombe a matsayin Jiha. Sannan zai tabbatar an cigaba da hakar man fetir Dan amfanin yankin da kasa baki daya.

Mai martaba sarkin ya yabi Dan takarar da cewa, yayi abubuwan masu kyau na kafa babban tarihi. Dalilin da yasa kenan ma mutanen yankinsa suke son sa da kasa baki daya.
A yayin yakin neman zaben, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani farfesa Isa Pantami Wanda ya wakilci shugaba Buhari, ya bukaci Al’umma da su zabi Tinubu da sauran yan takarar jam’iyyar APC.
Pantami kuma ya gayawa magoya baya cewa, su yi watsi da zargin da ake yadawa na cewa Shugaba Buhari baya goyon bayan Bola Tinubu.