Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, yayi alkawarin zai saka kimanin Dala Biliyan 10 Dan bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Sannan yayi alkawarin farfadowa da kuma sake gina tashar jirgin ruwa ta Calabar, idan har ya zamo shugaban kasar Najeriya.
Yayi wannan alkawarin ne a filin wasa na EU Esuene a Calabar, a jiya Litinin a jawabi ga magoya baya yayin babban gangamin yakin neman zabensa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Atiku yayi alkawarin fifita cigaban tashar jirgin ruwa ta Calabar Dan bunkasa tattalin arzikin jihar, da kuma Samar da karin ayyukan yi.

Atiku ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa zata sanya kimanin Dala Biliyan 10 ga tattalin arziki, wanda zai bawa matasa maza da mata damar fara kananan kasuwanci.
A nata bangaren, matar Dan takarar Atiku Abubakar wato Titi Abubakar ta fadi cewa, idan aka zabe su mijinta zai yaki talauci a tsakankanun mata da matasa.
Ta bayyana hakanne a wani taron ganawa da sauran matan jam’iyyar PDP, a jihar ta Cross River.