Babban kotun ƙoli ta ƙasa a Najeriya ta sanya ranar 22 ga watan Fabrariru domin cigaba da sauraron ƙarar da aka shigar gabanta na daina karɓar tsofaffin kuɗi.

A zaman kotun na yau da ake sa ran za yanke hukunci, Alƙalan da ke sauraron shari’ar sai dai ta dakatar da dokar hana karɓar tsaffin kuɗi.
Gwamnatin tarayya ta da babban bankin Najeriya CBN ne su ka saka dokar haramta amfani da tsaffin kuɗi na naira 200, 500, da kuma naira 1,000.

Ko a jiya Talata sai da gwamnan bankin Najeriya CBN ya sake jaddada matsayarsu kan cewa sun hana bankunan ƴan kasuwa karɓar tsofaffin kuɗi tun daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Wasu gwamnoni a Najeriya ne su ka shigar da ƙofarin gaban kotun ƙolin tare da ƙalubalantar sabon tsarin gwamnatin tarayya.