Gwamnan babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya bai’wa dukkan bankunan ‘yan kasuwa izinin ci gaba da karbar tsofaffin kudade wanda bankin na CBN ya dakatar a baya.

Daraktan Sadarwa na bankim Osita Nwanisobi ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a

Osita ya ce bankunan za su dinga karbar kudaden ne daga naira 500,000 zuwa abinda yayi kasa.

Daraktan ya kara da cewa bankin ya canja shawarar cewa dukkan mai tsohon kudi sai ya kai bankin CBN sannan za a karba.

Idan baku manta ba dai al’ummar kasar na kokawa sakamakon rashin karbar tsofaffin kudi da bankunan ‘yan kasuwa ba sa yi.

Yayin da sabbin kuma su ka yi karanci a cikin mutane wanda hakan ya haifar da talauci tsakanin mutanen kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: