Hukumar ƴan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa jami’anta sun cafke wata mata mai safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar.

Hukumar ƴan sandan tace ta cafke matar mai suna Fatima Sani, bisa zargin ta da hannu wajen safarar makamai ga wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar.
Da yake magana da ƴan jarida a ranar Juma’a, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, yace an cafke wacce ake zargin ne bayan an samu bayanai kan laifukan da take aikatawa.

Ya ce ranar 13 ga watan Fabrairun 2023, jami’an ƴan sanda sun cafke Fatima Sani ɗauke da harsasai guda 325, bayan an samu bayanin cewa tana ɗauke da kayan daga Lafia na jihar Nasarawa domin kai wa wani ƙasurgumin ɗan bindiga dake ɓoye a dajin Zamfara.

A yayin da take amsa tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ta daɗe a cikin wannan baƙar harkar, sannan ta taɓa kawo harsasai guda dubu ɗaya na bindigar AK-47 da bindigu guda uku ƙirar AK-47 ga ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Haka kuma ƴan sandan jihar sun cafke wasu masu garkuwa da mutane ciki har da wanda ya kitsa yadda aka sace mahaifiyar sa.
Muhammad Shehu ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a tura wacce ake zargin zuwa gaban kotu.