Fitaccen malamin addinin musulunci Sheik Ɗahiru Usman Bauchi ya umarci magoya bayansa da su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a babban zaɓe mai zuwa.

Malamin ya aike da saƙon ga magoya bayansa kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Ya ce ba za su goyi bayan mutanen da su ka ce za su ɗora daga inda aka tsaya ba, domin ba su ji daɗin inda aka tsaya ɗin ba.

Fitaccen malamin wanda ya shahara kuma ke ɗauke da magoya bayan masu tarin yawa, ya nuna matsayarsa yayin da ya rage kwana biyu kacal a gudanar da bvabban zaɓen shekarar 2023 a Najeriya.
