Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasara a zaben shugaban kasar Najeriya 2023.

 

Asiwaju Tinubu ya samu wannan nasara ne bayan samun mafi rinjanyen kuri’u a zaben jihohi 36 da birnin tarayya Abuja da akayi ranar Asabar, 25 ga Febrairu, 2023.

 

Tinubu wanda ya lashe zabe a jihohi 12 ya samu jimillar kuri’u 8,794,726 inda wanda ke biye masa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya lashe jihohi 12 da kuri’u 6,984,290 yayinda Peter Obi na jam’iyyar LP ya lashe jihohi 12 da kuri’u 6,101,533.

 

Shugaban hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana cewa

 

Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC bayan samun kuri’u mafi rinjaye da cika sharuda na doka ya zama zababben shugaban kasar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: