Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya bayyana cewa zai magance matsalar tsaron dake addabar kasa Najeriya kafin ya sauka daga kan karagar mulkin sa.

ya bayyana haka a jiya Juma a yayin da yaje babbar helkwatar sojin kasa Najeriya a yayin da yake rabawa jami a sojin Najeriy wasu daga cikin kayan aiki a babban birnin tarayyar Abuja.
Buhari ya ce zai yi nasara akan duk wata matsalala rashin tsaro a Najeriya da taki ci taki cinyewa kafin ya fita daga ofishinsa .

ya ce babu abin zai hana ba a magance tsaron Najeriya kafin karewar waadinsa, kuma za a yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da wannan kudrin cikin yan lokutan da suka rage.

Buhari ya ci gaba da cewa yana mai alfahari da tsawon shekarunsa bakwai na karagar mulki sun yi nasara akan kungiyoyin ta’adanci kamar su boko haram da ma wasu yan ta’adan dake damun kasa bakii daya.
sannan ya ce yana mai kara jinjinawa rundunar sojin najeriya bisa jajircewar da ta keyi akan sha’anin tsaro da irin gudumar da suka bada wajen dakile duk wata tashin tashina a lokacin zabe.
ya ci gaba da cewa yana da tabbacin zai magance duk wata matsalla ta tsaro tare da yin nasara kafin ya fita daga gidan gwamnatin Najeriya duk da saura kwanaki kadan.