Hukumar tsaron ciki a Najeriya ta DSS ta bayyana cewa akwai wasu mutane da ke shirin tayar da hankula a wasu sassan kasar a zaben gwamnoni da ke tafe a ranar 18 ga wannan wata.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ya fitar a jiya laraba, sanarwar ta gargadi mutane ko kungiyoyi da su guji yin duk wani abu da zai iya tayar da hankula domin kaucewa fushin hukuma.
Hukumar ta ja kunnen ‘yan siyasa da su zama masu bin doka da oda a daidai lokacin da a’ummar Najeriya ke shirin fita domin kada kuri’unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar asabar 18 ga watan Maris.

DSS ta jajjada cewa ta shirya tsaf domin kare ‘yan Najeriya da ke da niyyar fita domin kada kuri’unsu.

Hukumar ta za su tabbatar sun yi aiki da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro wajen dakile duk wani yunkuri na kawo tashin hankali a lokacin zabe.