Aƙalla masu iƙirarin jihadi 30 aka kashe yayin da aka kama mabiyansu sama da 900 a jamhuriyar Nijar.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen da su ka haɗa da mata daa ƙananan yara waɗanda su ka yi gudun hijira sanadin rikici tsakanin Boko Haram da ƙungiyar ISWAP.

Rundunar tsaron hadin gwiwar wasu ƙasashen Afrika da su ka haada da Najeriya Nijar da Chadi ne su ka kama mutanen waɗanda su ke zargi iyalai ne ga Mayaƙan Boko Haram.

Mutane talatin ake zargi an kashe a faɗan tsakanin kungiyoyin biyu.

Babban mai magana da yawun rundunar sojin kasar Chadi Laf Kanal Kanarudden Adegoke ya tabbatar da haka.

Ya bayyana a wata sanarwa da fitar a yau Laraba.

Ya ce tuni aka faara duba mutanen da aka kama, saannan su na ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

Mutanen da aka kama da su ka hada daa mata daa kananan yara sun kai su 960.

Leave a Reply

%d bloggers like this: