Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ɗage aikin ƙidaya a ƙasar zuwa watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakaa yau a Abuja.
Lai Mohammed ya ce za a yi aikin kidayar yan ƙasar a watan Mayu maimakon 29 ga watan Maris.

Lai Mohammed ya bayyana haka yau jim kadan bayan zaman majalisar zartarwa wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Shugaban hukumar ƙidaya a Najeriya ya tabbatar da cewar aikin kidayar za a yi har a dajin sambisa.
Ko a da a maya sai da ƙungiyar kare haakkin musulmi a Najeriya ta bukaci a ɗage aikin kidayar zuwa gaba ganin yadda watan Ramadan ke tunkarowa.