Hukumar gudanarwa ta kwalejin kimiyya da kere-kere da ke Jihar Kogi wato Kogi Poly ta kori wasu manyan malamanta guda hudu bisa laifin aikata lalata da wasu dalibai mata da wasu laifuka.

 

Mai magana da yawun kwalejin Uredo Omale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a garin Lokoja.

 

Daga cikin sauran laifukan da ake tuhumar malaman da su sun hada da rashin ladabi da rashin zuwa aiki da saba doka amfani da takardun bogi da kuma karkatar da wasu kudade.

 

Kakakin ya ce daga cikin malaman akwai mutum biyu da su ka yi amfani da wasu takardun bogi wajen karbar tallafi har naira miliyan 22.6 da kuma naira miliyan 21.2 domin samun horo a kasar waje,inda su ka cinye kudaden ba tare da sun je ba.

 

Uredo ya kara cewa an kafa kwamitin da zai yi aikin bincike akansu, ya ce kwamitin ya bukaci hukumar kwalejin ta bi duk hanyoyin doka domin karbo kudaden.

 

Sannan ya bayyana cewa akwai wadda aka kora sakamakon rashin zuwa aiki na tsawon watanni shida tare da umartar ta da ta dawo da albashin da ta karba na tsayin lokacin da ba ta zuwa aiki.

 

Kakakin ya ce hukumar kwalejin ta kuma yiwa wasu malamai takwas karin girma daga matakin kananan malaman kwaleji zuwa manyan malamai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: