Akalla mutane hudu ne su ka rasa rayukansu a yayin wani rikici da ya barke tsakanin tawagar gwamnan Jihar Kano Malam Nasir El’Rufa’i da kuma mabiya addinin Shi’a.

 

Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Alhamis a lokacin da gwamnan ya kai ziyara unguwar Bakin Ruwa da ke Jihar.

 

Jami’an tsaron tawagar ta gwamnan sun budewa mabiya darikar shi’a wuta ne a lokacin da su ka fara jifan tawagar gwamnan a ziyarar da ya kai yankin.

 

Tawagar ta gwamnan sun yi arangamar ne a lokacin da mabiya addinin na shi’a ke taron su na mako-mako a unguwar.

 

Wani shaidar gani da ido Tasiu Muhammad ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan shi’ar sun fara yiwa tawagar gwamnan ihu a lokacin da su ke kokarin wucewa ta cikinsu.

 

Dan uwan daya daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu ya ce dan uwansa da aka kashe ba d’an shi’a bane direban mota ne harsashi ya sameshi.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’an tsaron sun kama wasu cikin matasan sun tafi da su.

 

A yayin da aka tuntubi wakilin ‘yan shi’a na Kaduna Abdullahi Usman ya bayyana cewa a cikin wadanda aka kashe babu mambobin kungiyar.

 

Ya ce wadanda aka kashe direbobin motar hayane da ke kusa da abin ya faru.

 

Sannan ya kara da cewa ba gaskiya ba ne mambobin su sun jefi tawagar gwamnan da duwatsu.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Muhammad Jalige ya ce da zarar sun kammala bincike zai fitar da sanarwa akan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: