Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa jirgin sama Mallakin Kasar wato Nigeria Air zai fara tashi kafin ranar 29 ga watan Mayu shekarar da muke ciki.

 

Ministan sufurin Jiragen sama Sanata Hadi Sirika ne ya tabbatar da hakan a gurin taron masu ruwa da tsaki akan harkokin sufurin jiragen sama a ranar Alhamis.

 

Sirika ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin tarayya na daukar matakan da su ka kama wajen magance matsalolin da kamfanonin Jiragen sama na cikin gida da su ka bujiro da su tare da zuwa kotu domin dakatar da gudanar da fara aikin jirgin.

 

Sanata Sirika ya ce matakin da kamfanonin jiragen sama na ‘yan Najeriya su ka dauka babu adalci a cikinsa,inda ya ce gwamnati mai ci a yanzu ta tallafawa kamfanoni fiye da gwamnatoci da su ka shude a baya.

 

Ministan ya kuma zarge su da kawo nakasu wajen tabbatar da kamfanin dillalai na Kasa wanda hakan zai yi tasiri wajen samar da ayyuka a cikin harkar.

 

Hadi Sirika ya kara da cewa ma’aikatar sufurin jiragen sama ta Najeriya itace daya tilo da fadin duniya da take da kwararrun matuka jirgin sama wadanda ba su da ayyukan yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: