Rundunar sojin Najeriya ta samu Nasarar kubutar da wasu mutune 201 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a Jihohin Borno da Kaduna.

Daraktan yada labaran rundunar Manjo Janar Musa Danmadami ya tabbatar da hakan a yayin wani zaman tattaunawa da hedkwatar tsaro ta Kasa ke yi duk makwonni biyu a Ranar Alhamis.

Jami’an sun samu nasarar bayan yin garkuwa da mutanen tsawon sati biyu da ya gabata a wani atisaye da su ka gudanar a Jihohin.

Danmadami ya kara da cewa jami’an atisayen Whirl Stroke sun hallaka ‘yan bindiga 14 daga bisani su ka kwato kayayyakim su 12 tare da kubtar da mutanen daga hannun su.

A yayin wata ziyara da babban jami’in da ke kula da shiyyar GOC 7 kuma kwamandan atisayen hadin kai Manjo Janar Waidi Shu’aibu ya kai ziyarar aiki bataliyar hadin gwiwa 112 da ke garin Mafa a Jihar Borno.

Janar Shu’aibu ya jinjinawa jami’an akan kokarin da su kayi na rushe wani shirin mayakan ISWAP da su ka shirya kai hari garin Mafa a ranar Lahadin da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: