Rundunar yan sandan jihar Edo ta tabbatar da yin garkuwa da wasu mutane biyar a karamar hukumar Edo ta yamma.

kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyana ya ce lamarin ya faru a ranar Alhamis.

SP Childi ya ce sun samu kiran waya daga wata mata ta ce mijinta da wani ma akacinsa sun ta fi gona domin girbe amfani sai wasu masu garkuwa wadanda su ka je gonar da yake aiki kusan su biyar tare da tafiya da su.

Ya ce wanda aka yi garkuwa da shi mai suna Bernard mai shekaru 52 da abokin aikinsa sun bar gida da nufin zuwa gona aiki a hanyar su ta dawowa ne suka hadu da yan garkuwa suka tare su da kama su zuwa cikin daji.

Sai dai kamar yadda iyalinsa ta bayyana ta ce wayarsa dai yanzu haka bata shiga.

Kakakin rundunar Child ya ce jami’an su sun shiga daji ba dare ba rana domin tabbatar da kubutar da wadanda ake zargi da sace mutanen.

Sai dai ya ce lamarin an tura shi zuwa ga babban sashen binceke domin tsaurara binceke da kubutar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: