Wasu da ake zargin jaman sojojin ne sun hallaka wasu iyalai uku a yankin Babana dake karamar hukumar Bogu ta jihar Naija.

mutanen uku da ake zargi an hallaka su ne kan hanyar su ta dawowa daga kasuwa abin ya faru.
shugaban karamar Borgu na jihar Naija Alhaji Sulaiman Yarima shi ne ya tabbatar da lamarin ga manema labarai.

Ya ce hatsarin ya faru a yankin Babana inda wasu daga cikin sojojin suka hallaka mutane uku lokacin da lamarin ya faru.

ya ce yana mai rokon doka ta yi aikinta bisa wannan abun da ya faru tun da kowa zaman doka yake yi, duk da cewa yarima bai bayyana yadda lamarin ya kasance ba.
sai dai da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Naija ya bayyana cewa wannan batu ne da ya shafi sojoji ba yan sanda ba.