Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane sun saki wata mata da mijinta da suka yi garkuwa da su bayan hallaka jaririnsu.

lamarin ya faru ne yankin Janjala dake karamar hukumar Kagarko a jihar kaduna.
Jaridar daily trust ta rawaito cewa wasu masu garkuwa da matane sun yi garkuwa da wani mai suna mustapha da matarsa mai dauke da juna biyu da karamar yarsu yar shekaru 16 a gidansu dake janjala a kaduna.

wani daga cikin yan uwan wadanda aka yi garkuwa da su mai suna Datti ya bayyana cewa masu garkuwa sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan biyu kafin sakin mustapha, sai dai bayan biya suka kara neman a ba su wata naira miliyan biyun domin sakin matarsa.

sannan ya ci gaba da cewa daga baya suka cewa sai an ba su naira miliiyan 1.5 kafin sakin karamar yarinyar.
Ya ci gabada cewa sun samu yawan kiran waya daga shugaban yan garkuwa da mutanen akan in ba a kawo ba sai sun hallaka wadanda suke hannun su.
Sai dai sun saki wadanda suka yi garkuwa da su din gaba daya amma sun hallaka jaririn wanda mai cikin ke dake da shi kamar yadda shugban yan garkuwa ya bayyana musu a wayar tarho.
Shima madakin garin janjala ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wannan abu ne mai tayar da hankali da taba zuciya kuma dole hukuma za ta dauki mataki akai.
Sai dai a yayin hada rahotan rundunar yan sandan jihar ta kaduna ba ta ce komai a kai ba.