Akalla maniyyyata aikin umara 20 ake zargin sun rasa rayukansu yayin da wasu 29 suka samu raunuka bayan wani hatsarin mota da ya faru a kasar Saudiya.

Lamarin ya faru ne a kasar ta saudiya a yayin da wata mota ta debo mutane wanda suke kan hanyar aikin umra ta yi karo da wata babbar mota.
Motar dai ta yi karo ne a yayin da take tafiya da wata babbar mota a kan hanyar ta zwa gudanar da aikin umara.

Bayan hakane ake bayyana cewa akalla mutane 20 ne suka rigamu gidan gaskiya inda 29 ke karbar kulawa a babban asibitin kasar kamar yadda aka rawaito.

Sai dai cikin rahoton ba a bayyana mutanen wacce kasa ne ba.