Wata kungiyar matasan Arewacin Najeriya Northern Youth Council of Nijeria ta gargadi gwamnatin tarayyar Najeriya akan yunkurin da ta ke yi na cire tallafin man fetur a kasar.

Shugaban Kungiyar Alhaji Isa Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Jihar Kaduna.


Alhaji Isa ya ce kungiyar ta bayyana tsoron ta saboda kada a samu wasu tsiraru su yi awon gaba da dukkan wani tallafin wanda zai rage radadin cire tallafin kamar yadda ya faru da tallafin cutar korona.
Kungiyar ta bukaci da gwamnatin tarayya da ta sake yin nazari akan batun cire tallafin na mai, wanda hakan ka iya karawa al’ummar kasar kuncin rayuwa.
Arewa Youth ta kuma bai’wa gwamnatin shawarar mayar da hankali wajen samarwa da mutanen kasar ayyukan yi wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar.
Sannan ta bayyana cewa akwai hukunci mai tsauri ga dukkan wanda yake son jefa al’ummar Najeriya cikin kuncin rayuwa matukar bukata ta dawo dashi lokacin zabe.
Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran kungiyoyi da su tashi tsaye wajen taya ‘yan Najeriya yaki akan hakan, inda ya ce ba za ta yarje da duk wani yunkuri na cire talkafin mai ba a ƙasar.