Hukumar jin dadin Alhazai reshen jihar kano ta bayyana cewa dukkan maniyyacin aikin hajji ya gaggauta biyan kudinsa na aikin kafin 21 ga watan da muke ciki.

Jaridar Daily trust a rawaito yadda shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano Alhaji Muhammad Saleh Danbatta ya bayyana a yau Asabar.
Ya ce dukkan wanda ya biya naira miliyan daya da rabi to ya gaggauta biyan sauran kudin da ake binsa kimanin dubu dari hudu nan da ranar 21 ga Apirilu.

Ya ce wannan na zuwa ne bayan hukumar jin dadin alhazai ta kasa ta bayyan karin kudin da ta yi har kusan miliyan uku mafi tsada a kudancin kasar.

Ya ce shi yasa aka bayyanawa Alhazan da su gaggawa wajen biyan karin da aka yi na kujera.
Ya ce amma hakan ya faru ne ba don komai ba sai don tsadar da haraji yayi a Najeriya da kuma kasa mai tsarki bayan tashin dala.
Ya ce bayan gama biyan kudin a ranar 21 ga watan da muke ciki na Apirilu to za kuma a fara gudanar da bita.