Ƙungiyar tattalin ƙasashen Afrika ECOWAS ta yi kira da a gaggauta dakin yara da aka sace a jihohin arewacin Najeriya.

An yi garkuwa da yara da mata a jihar Zamfara a makon da ya gabata.
Kungiyar ta yi Alla-wadai da harin da aka kai jihohin Zamfara da Benue wanda aka kashe mutane sama da 70.

Ana zargin an yi garkuwa da yara sama da 80 a Zamfara wanda masu garkuwan su ka bukaci a basu naira 20,000 kuɗin fansar kowanne daga ciki.

A yan kwanakin nan masu garkuwa da mutane sun matsa da kai hare-hare musamman a jihohin arewacin Najeriya.
Ko da yake rundunar tsaron kasar ta sha alwashin murkushe duk wani aikin ta’addanci a kasar.
Samar da tsaro na daga cikin manufar gwamnatin shugaba Buhari, wanda ya rage ƙasa da watanni biyu ya yi adabo da mulkin ƙasar.