Rundunar ƴan sanda a jihar Delta sun kama mutane uku kan zargin hallaka wani ɗan siyasa a jihar.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Bright Edafe ne ya tabbatar da haka ya ce an kama waɗanda ake zargin mutum uku a ranar Talata.

An hallaka fitaccen ɗan siyasar ne a ranar Lahadi a gidansa, yayi da mutanen su ka harbeshi.

Kakakin ƴan sanda a jihar ya ce su na ci gaba da bincike a kan mutane uku da su ka kama.

Tuni jam’iyyar APC a jihar ta yi kira da a gaggauta bincike a kai tare da gurfanar da waɗanda su ka aikata hakan a gaban kotu.

Wanda aka kashe mai suna Sylvester Efeurhobo jigo ne a siyasar ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: