Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Yobe ta ayyana Ibrahim Bomai a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan mazabar Yobe ta Kudu a majalisar dattawa.

A cewar sakamakon zaben na yau Asabar 15 ga watan Afrilu, baturen zabe, Abatcha Melemi ya bayyana cewa, Bomai na APC ya samu kuri’u 69,596, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Halilu Mazagane da ya samu kuri’u 68,885.


Tun farko, hukumar zabe ta dakata da tattara sakamakon zaben yankin tare da ayyana shi ‘inconclusive’ saboda wasu dalilai na aringizon kuri’u a rumfunan zaben Manawachi a karamar hukumar Fika.
Daga baya, an sanar da cikon zaben a yau Asabar don karasa zaben daga inda aka tsaya a watan Faburairun da ya gabata.
Da yake sanar da manema labarai sakamakon zaben, baturen zaben ya ce abin da ya fada gaskiya ne kuma shi ne adalci.