Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi yafiyar al’ummar Najeriya a lokacin da wa’adin mulkinsa ke shirin karewa a watan gobe.

Bubari ya nemi afuwar ne a lokacin da kungiyar Mazauna birnin Abuja suka kaimasa ziyarar barka da sallah a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.
Shugaban ya godewa Allah bisa nimamin da ya yi masa, acewarsa yayi gwamna yayi Minista kana yayi shuganan kasa a tarayyar kasar.

Sannan ya bayyana hakan da cewa babbar nima ce da ga Allah.

Akarshe Shugaba Buhari ya jinjinawa al’ummar kasar bisa juriya da suka nuna a lokacin mulkinsa.