Fitaccen ‘dan siyasar nan kuma daya daga cikin jagorori a jam’iyyar APC, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, ya yi kira ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

 

Alhaji Abdulmajid wanda aka fi sani da Danbilki Kwamanda, yana so zababben shugaban kasar ya ajiye batun zawarcin Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam”iyyar APc.

 

Dan siyasar yana zargin Bola Ahmed Tinubu yana kokarin mayar da Rabi’u Musa Kwankwaso cikin jam’iyyar APC, yace hakan ba zai taimaki jam’iyyarsu ba.

 

Danbilki Kwamanda ya yi wannan bayani da ya zanta da manema labarai jiya a garin Kano.

 

A cewar Kwamanda, sun gano zama da za ayi a asirce tsakanin shugaba mai jiran gado da kuma tsohon Gwamnan Kano da ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP.

 

Idan aka yi nasarar karkato da hankalin Rabiu Kwankwaso har ya sauya-sheka, hakan zai yi wa jam’iyyar APC illa a matakin jiha da kasa, a cewar ‘dan siyasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: