Wata babbar kotu da ke zamanta a Jihar Adamawa ta yi zama akan Shari’ar wasu magoya bayan jam’iyyar PDP wadanda jami’an tsaron DSS su ka Kama a Jihar.

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa a yayin zaman an hango Alkalin kotun Christopher Dominic Mapeo ya bai’wa jami’an tsaron DSS da suka Kama mutunan umarnin fito da mutanen ba tare da bata lokaci ba.

A yayin zaman da ya gudana a ranar Alhamis Alkalin ya bayyana cewa matukar hukumar bata fito da mutanen ba ta sabawa doka.

Alkalin ya dage sauraren Shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Mayu 2023 domin jin ta bakin wadanda ake kara a gaban kotun.

An shigar da karar neman sakin mutanen su uku ne tun a ranar 20 ga watan Afrilun da muke ciki bayan da Chif L. D Nzadon ya shigar da karar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: