Aƙalla mutane 40 ƴan bindiga d ka hallaka a wasu kauyuka jihohin Kebbi da Sokoto.

Akwai mutane 36 da aka kashe a garin Daan Umaru ƙaramar hukumar Zuru ta jihar Kebbi, wanda kuma daga ciki akwai jami’an yan sanda shida.

Tuni aka sallaci mutane 27 yayin da aka samu wasu da dama da su ka samu munanan rauni.

Haka kuma akwai wasu mutane da aka yi garkuwa da su a wasu ƙauyuka.

Haka kuma akwai mutane uku da aka kashe a wani kauyen ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Duk da cewar yan sanda a jihar ba su ce komai a kan lamarin ba.

Ana ci gaba da samu ƙaruwar kai hare-hare a wasu jihohin arewacin Najeriya tun bayan kammala babban zaɓe a Ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: