Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasa Najeriya NCDC ta ce mutane 154 ne suka mutu sakamakon cutar zazzabin lassa.

 

Sanarwar da fito daga hukumar ta NCDC a jiya Litinin ta ce akalla mutane 154 ne suka rasa rayukansu a farkon wannan shekarar ta 2023.

 

NCDC ta ce bayan mutuwar mutane 154 akalla an samu yawan masu kamuwa da cutar 897 a jihohin 26 a cikin watanni hudu.

 

Jihohin da suka hada Bauchi, Benue, Ebonyi, Enugu, Gombe, Jigawa, Kano, kogi, Taraba, Nassarawa, filato da dai wasu sauran jihohin kasar.

 

Sannan yawancin jihohin da cutar tafi tsamari sune Ondo, Edo, da kuma jihar Bauchi.

 

Rohotan ya nuna cewa adadin masu dauke da cuta a wannan shekarar ya haura na bara.

 

Cutar zazzabin lassa wadda ake samun ta daga jikin bera ta yi saurin yaduwa a kasar tun bayan bayan bullarta a farkon shekarar 2022 inda ta harbi jama a dama da kuma hallakarwa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: