Zaɓaɓɓen shugaban Kasar Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yaba tare da jinjinawa marigayi shugaban Kasar Najeriya Umaru Musa ‘Yar Aduwa bisa jajircewarsa a kan Damokuradiyya da shugabanci nagari.

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a tare da alkawarin yin koyi da marigayin a lokacin mulkinsa.


A yayin jawabin tunawa da ranar mutuwar marigayin wadda aka gudanar a ranar Juma’a Bola Tinubu ya ce Umaru Musa ‘Yar Aduwa yayi rayuwa mai cike da amfani.
Tinubu ya bayyana cewa zai yi koyi da kyawawan misalan da shugabanni irinsu ‘Yar Aduwa da su ka bari akan sadaukar da kai a Najeriya.
Umaru Musa ‘Yar Aduwa ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010 da ta gabata ya na tsaka da shugabancin ƙasar.