Hukumar Aikin Hajji a Kasa (NAHCON) ta daidata da kamfanonin jiragen sama hudu na cikin gida da aka ba wa kwangilar jigilar maniyyata a aikin Hajjin da ke zuwa.

 

Bangarorin sun daidaita ne bayan a makon jiya kamfanonin sun ki sanya hannu kan yarjejeniar aikin saboda yakin kasar Sudan da ke bukatar su sauya hanyar jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya, lamarin da zai kara wa tafiyar tsawo.

 

A kan haka ne wakilan kamfanonin suka ki sanya hannu kan yarjejeniyar aikin, bisa hujjar cewa karin tsawon tafiyar zai kara yawan kudaden da za su kashe, don haka suka bukaci karin kudin jigilar maniyyatan.

 

Amma, shugaban hukumar, Hassan Zikrullah Hassan, ya ce, a zaman da aka sake yi ranar talata a ofishinn NAHCON da ke Abuja, kamfanonin Aero Contractors da Air Peace da Azman Air da kuma Max Air sun amince sun sanya hannu kan yarjejeniyar da suka ki amincewa da farko.

 

Idan baku manta ba a baya an kawo rahoton cewa kamfanonin jiragen sun ki amincewa da yarjejeniyar kafin wannan lokacin.

 

 

 

 

 

Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, ta dage shari’ar da tsohon dan majalisar nadin sarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad ya bukaci a tube rawanin Nuhu Bamalli daga sarautarsa ta Sarki.

 

Muhammad wanda shi ne tsohon Wazirin Zazzau kuma yana daya daga cikin wadanda suka nada Sarki Bamalli, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu mutane 13 a kotun, yana neman a tube rawanin Sarkin Zazzau na 19.

 

Daga cikin ragowar mutum 13 da ake kara har da Sarki Ahmed Nuhu Bamalli da marigayi Limamin Kona, Malam Sani Aliyu wanda ya riga mu gidan gaskiya a watan Yullin 2021.

 

Bamalli wanda tsohon Jakadan Najeriya ne a kasar Thailand, an nada shi Sarkin Zazzau na 19 a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020.

 

Nadin sarautar wanda Gwamna Nasiru El-Rufai ya yi na zuwa ne bayan Majalisar nadin sarki ta bayyana amincewarta.

 

Sai dai wanda ake kara sun yi watsi da bukatar a zaman kotun wanda Mai Shari’a Isah Aliyu ya jagoranta, suna masu cewar mai karar ba shi da hurumin gabatar da wannan bukata ta kalubalantar rawanin Sarki Bamalli.

 

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan zaman kotun, lauyan Masarautar Zazzau, Abdul Ibrahim (SAN), ya ce suna kalubalantar karar ce la’akari da cewa mai ita ba ya cikin ko daya daga cikin wadanda gidajen da za su iya gadon sarautar ta Zazzau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: