Jami’an yan sandan Jihar Anambra sun sami nasarar kashe ‘yan bindiga biyu tare da kama wasu ‘yan fashi da makami.

Hakan na zuwa ne biyo bayan aikin hadin gwiwa da ‘yansandan suka gudanar tare da ‘yan banga, kamar yadda kakakin yan sandan jihar ya sanar a yau Talata.


Wadannan ayyukan hadin gwiwa sun samar da babban ci gaba mai kyau a ranar Lahadi 7 ga watan mayu da misalin karfe 8:45 na dare.
Ya ce ‘Yan sandan da ke sintiri a Usmusiome Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa sun kama wasu gungun mutane hudu da ke aiki a cikin wata mota kirar Lexus SUV da ba ta da rajista, inda suka kwato wasu bama-bamai guda biyu, bindiga kirar AK-47 daya, harsashi masu dangon 7.62, laya da sauran abubuwa a hannunsu.
Ya kara da cewa a lokacin da jami’an suke artabu da ‘yan bindigar sun kashe biyu daga cikin ‘yan kungiyar, yayin da wasu biyu suka tsere.
Tuni dai aka fara kokarin kamo sauran ‘yan kungiyar da suka gudu.
Sannan ya ce, jami’an ‘yansanda a Azu Ogbunike, a yankin karamar hukumar Oyi a jihar Kudu-maso-Gabas, sun cafke wasu ‘yan fashi da makami guda hudu a yayin da suke lalata wata babbar mota da ake zargin ta sata ce.