Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kuma shugaban gwamnonin Jam’iyyar PDP yayi hasashen hukuncin da Kotu za ta yanke akan zaben shugaban Kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

 

Tambuwal ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja a gurin wata liyafa da kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta PDP ta shiryawa gwamnoni masu Jiran gado da wanda wa’adinsu ya kusa karewa.

 

Aminu Tambuwal ya ce yana da kwarin gwiwa Kotu za ta maida wa dan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar hakkin sa na zama shugaban Kasa kamar yadda kudin tsarin mulki kasa ya Tanada.

 

Tambuwal ya kara da cewa su na da yakinin mulki zai dawo Hannun Atiku Abubakar, inda ya ce a halin yanzu su na kallonsa ne a matsayin shugaban kasa mai Jiran gado.

 

A nasa bangaren Alhaji Atiku Abubakar a yayin liyafar ya shaidawa mahalatta Liyafar cewa jam’iyyar PDP za ta karbo nasararta sakamakon jam’iyyar ba ta badi ba a zaben da aka gudanar na shugaban kasa.

 

Jagororin jam’iyyar ta PDP sun bayyana cewa Shari’a ce kadai gatan mara gata a Najeriya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: