Zababban gwamnan Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana dalilian da ya sanya bai shirya murnar da ya samu ba bayan ya samu nasara a Zaben da aka gudanar na shekarar 2023.

Uba Sani ya bayyana cewa yaki shirya taron ta yashi murna ne saboda ya maida hankali akan nauyin da mutane Jihar su ka dora masa a matsayin sa na Sanatan Kaduna ta Tsakiya.

Zababban gwamnan ya tabbatar da hakan ne a yayin wata fira da aka yi dashi a Jihar,daga bisani kuma ya musanta jita -jitar da ake yadawa cewa bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe ya bar Jihar ta Kaduna.

Sani ya kara da cewa ba dabi’ar sa ba ce ya shiga irin wadannan shagulgulan na zamani wanda ‘yan adawa su ke tsammani ,inda ya ce hakan ba daidai ba ne.

Sabon gwamnan ya kara da cewa mai makon shirya irin wadannan shagulgulan malam Addinin Musulunci da na Kirista su ka yi masa Addu’o’in neman taimakon Allah a yayin mulkin nasa.

Sannan ya ce zai yi tafiya da kowanne bangare na musulmi da kiristoci na Jihar daga lokacin da aka rantsar dashi a ranar 29 Mayu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: