Ƙungiyar Fiulani makiyaya a Najeriya MACBAN ta ce ta rasa mambobinsu makiyaya fiye da 100 a ƙauyukan ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Shugaban ƙumngiyar a jihar Filato Nuru Abdullhi ne ya sanar da haka a wata sanarwa ya ƙungiyar ta fitar.
Ƙungiyar ta ce aƙalla makiyaya da mata da yara sama da 200 su ka rasa a a harin da aka kai ranar Talata makon jiya a jihar.

Sanarwar ta ce makiyaya sama da 100 aka kashe cikin daji a jihar yayin da su ka rasa mata da yara kananan sama da 200 wanda su ka yi Ala-wadai da kisan gillar da aka yi wa mambobinsu.

Sanarwar ta ƙara dacewa akwai dabbobi da su ka haɗa da shanu, tinkiyoyi da akuyoyi da su ka rasa a ƙauyukan da ke tsakanin ƙananan hukumomin Mangu da Riyom a jihar.
Haka kuma sun buƙaci jami’an tsaro da su taimaka wajen gano gawrwakin da aka rasa na mambobin ƙungiyar da aka hallaka.
Sannan sun buƙaci gwamnati da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da ma hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa da sauran masu ruwaa da tsaki da su shigha lamarin don ganin hakan ba ta sake faruw ba tare da duba halin da aka sanya mutanen a ciki.