Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’Rufa’i ya gayyaci tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Rabi’u Musa Kwankwaso domin ya kaddamar da ayyukan da gwamnatin sa ta kammaala a Jihar.

A yau juma’a tsohon gwamnan na Kano zai kaddamar da ayyukan gwamnatin ta Kaduna.
Hadimi ga tsohon gwamnan Ibrahim Aminu shine ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.

Hadimin ya ce daga cikin ayyukan da kwankwaso zai kaddamar akwai Sabuwar zama da ke Unguwar Rimi a Jihar da titin Emir Road da kuma titin School Road da gwamnan Jihar ta Kaduna ta kammala.

Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya isa Jihar ta Kaduna ne a yammacin ranar Alhamis bayan kammala jagorantar wani taro na musamman a garin Minna da ke Jihar Neja akan rantsar da gwamnatin Jihar.