Shugaban matan jam’iyyar APC Betta Edu ta bayyana cewa shugaban kasa Mai jiran Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai yiwa ‘yan Najeriya aiki tukuru wanda hakan zai sanya ‘yan Kasa su roke shi ya koma wa’adi na biyu.

Edu ta tabbatar da cewa ya zuwa yanzu Tinubu ya riga da ya gama tsara abubuwan da ya ke son cimmawa a cikin kwanaki 60 na farkon mulkin sa tun daga ranar 29 ga watan Mayu.
Shugabar jam’iyyar ta bayyana cewa Tinubu ya riga da ya shirya tsaf domin cike dukkan guraben da gwamnatin shugaba Buhari ta bari.

A cikin wata fira da aka yi da ita a gidan Talabijin na Channels ta bayyana cewa shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa zai mika Najeriya a hannun wanda zai dora daga inda ya tsaya kuma zai yi aiki fiye da wanda yayi a gwamnatinsa.

Edu ta Kara da cewa ya kamata ‘yan Najeriya su fahimci cewa a koda yaushe Najeriya ci gaba ta ke bata tsayawa.
Sannan ta ce gwamnatin Tinubu za ta fara gudanar da ayyukan ta tun daga ranar da aka rantsar da ita.