Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sha rantsuwar fara aiki a matsayin shugaban Najeriya na 16.

Tinubu da aka rantsar a matsayin sabon shugaban Najeriya ya karbi rantsuwar fara aiki yau a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.
Manyan baƙi da attajirai a ciki da wajen Najeriya ne su ka halarci taron.

Daga cikin waɗanda su ka halarci taron har da tsaffin gwamnonin Najeriya da su ka kammala mulkinsu.

Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaro sun dakatar da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai ɗakinsa daga shiga wajen da aka warewa manyan baƙi.
Bola Ahmed Tinubu ya kasance shugaban Najeriya na 16 bayan shan rantsuwa a yau tare da karɓar ragamar mulkin ƙasar daga hannun tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
An yin faretin girmamawa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima.