Sabon gwamnan jihar Kano Injiya Abba Kabir Yusif wanda ka fi sani da Abba Gida-Gida ya bayyana cewa ya soke ciniki da aka yi na siyar da kadarorin gwamnati a lokacin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.

Da yake jawabi a jiya Talata bayan rantsuwa Abba ya ce mutanen da suka sa yi kadarorin gwamnati sun soke wannan ciniki.

Ya ce kamar yadda gwamnatin tsohon gwamna Ganduje ta sayar da wuraren da malakin ne na gwamnatin kano.

Ya ce gwamnatin kano ba za ta yarda da wannan tsarin ba kuma ya na mai cewa wannan ciniki ba kuma ya warware shi.

cikin kadarorin da ake zargi an sayar sun hada da masallatai makabartu filayen makaranta da kuma gefen badala.

ya ce za kuma a ci gaba da bincike akan wadansu abubuwan da aka yi gwamnatin Ganduje ta yi don kuwa dole a bincike ta wato ba za dora akan abinda Ganduje ya bari ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: